Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotun Brazil Ta Ce A Ci Gaba Da Garkame Tsohon Shugaban Kasar


Luiz Inacio Lula da Silva tsohon shugaban kasar Brazil zai ci gaba da zama gidan kaso
Luiz Inacio Lula da Silva tsohon shugaban kasar Brazil zai ci gaba da zama gidan kaso

Jiya Lahadi wani alkali ya yanke hukumcin sakin tsohon shugaban amma alkali Sergio Moro da ya daure shugaban bisa ga samunsa da laifin cin hanci da rashawa ya ce kotun bata da ikon sakinshi

Wata kotun daukaka kara a kasar Brazil ta bada umarnin a ci gaba da garkame tsohon shugaban kasar Luiz Inacio Lula Da Silva a gidan yari, ta canja hukuncin da wani alhaki a wannan kotun ya yanke, tunda farko a jiya Lahadi cewa a saki tsohon shugaban.

Alkali Sergio Moro wanda shine ya yanke hukuncin daurin da aka yiwa tsohon shugaban a watan Afrilu bisa samunsa da laifin ci hanci da rashawa, yace kotun daukaka karan bata da ikon sakin tsohon shugaban, dan siyasa mai farin jinni a kasar sosai.

Duk da hukuncin daurin shekaru goma sha biyu da aka yanke masa a bara, tsohon shugaba Lula yana da farin jinni a kasar. Kdiddiga da aka yi ya nuna cewa, idan tsohon shugaban ya sake tsayawa takara, zai iya lashe zabe a karo na uku a zaben da za’a yi a watan Oktoba.

Ya ja ragamar mulkin Brazil daga shekara ta dubu biyu da uku zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha daya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG