Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kungiya Daga Amurka Ta Kwashe Shekaru 25 Tana Taimakawa Mata A Kasar Nijar


Tambarin Jamhuriyar Nijar

A birnin Kwanni cikin jihar Tawa, aka gudanar da bikin cika shekaru ishirin da biyar da kungiyar da ta samo asali daga Amurka ta yi tana taimakawa mata ta fannoni daban daban a kasar ta Nijar.

Kungiyar tana taimakawa mata da basussuka, da yaki da jahilci da kiwon dabbobi da aikin noma, da raya kasa, da kiwon lafiya duk a domin yaki da fatara da talauci.

A cewar gwamnan jihar Tawa da ya jagoranci bikin tare da magatakardar gundumar birnin Kwanni da sarakunan gargajiya da magajin gari da manyan ma'aikatan jihar da mata da suka yi dafifi a wurin, yace wannan abin alhari ne ga kasar. Yace mata dubu goma sha biya akan basu dubu dari uku. Abu ne da yakamata kowa ya yi koyi dashi.

Shugabar ma'aikatar dake kula da tsarin na mata Dr. Fatima Zainu tace tsarin na taimakawa maza da mata musamman abubuwan da suka shafi kananan sana'o'i da lura da wasu matsaloli da suka shafi mata idan mutane suka hada kansu suna iya shawo kan matsalolin da suka addabesu.

Malam Yahuza dake wakiltan shugaban kungiyar a birnin Kwanni yace wannan fasaha da kungiyar ta kirkiro a halin yanzu ta yadu duk fadin duniya. Yace bayan kungiyar ta kai jihohi takwas a kasar Nijar wasu kasashe da dama sun zo su koyi abun da kungiyar ke yi. Kasashe kaman su Mali da Ivory Coast da Burundi da Uganda tare da wasu kasashen Turai sun kai tsarin kasashensu. Yace kungiyar ta taimaka mata sun bunkasa abun hannunsu. Yace yayinda suka soma wasu basu da komi. Yanzu mata har da gonaki suke saye.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG