Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kungiya Tana Yunkurin Yaki Da Zazzabin Cizon Sauro


Sauro da yake kawo ciwon zazzabi
Sauro da yake kawo ciwon zazzabi

Wata kungiyar masanan yadda na’ura mai kwakwalwa (koputa) ke aiki sunce sun sarrafa wata mahimmiyar na’urar da ke iya karya lagon zazzabin cizon sauro.

Wata kungiyar masanan yadda na’ura mai kwakwalwa (koputa) ke aiki sunce sun sarrafa wata mahimmiyar na’urar da ke iya karya lagon zazzabin cizon sauro. Wannan labarin ya biyo bayan kididdigin kwanannan da ke nuna cea daga cikin milyan 300 – 500 na masu kamuwa da zazzabin cizon sauro, mutane milyan daya ke mutuwa inda kuma Nijeriya take da mutane fiye da 300,000 dake mutuwa sakamakon zazzabin cizon sauro a kowace shekara.

Masanan da aka fi sani da Mobile Software Solutions Limited wata kungiyar masana fasahar sadarwa ce ta Nijeriya wadda take fuskantar kalubalan da zazabin cizon sauro yake yi a kasar Nijeriya inda suka kirkiro wata na’ura da suke kira “Malaria Destroyer Game” (MDG) watau wasan lalata zazzabin cizon sauro wanda zai iya shafar fiye da mutane milyan 50 a Nijeriya da kuma fiye da mutane milyan 500 a Afrika.

Wannan wasan wani fannin fasaha da ilimi ne wanda aka kafa bisa na’aurar fasaha ta kwamputa wadda aka kirkiro domin kare zuriya masu zuwa a Nijeriya da kuma Afrika ta wurin kawas da sauro wanda kuma zai haifas da kawas da zazzabin cizon sauro.

Cikin yan kwanakin nan Ministan lafiya, Prof. Onyebuchi Chukwu, ya baiyyana cewa a kowanne minti 45, yaro daya yana mutuwa sakamakon zazzabin cizon sauro a Afrika, wanda ke kai ga asarar dala biliyan 12 na dukiya kowace shekara, yanayin da ya baiyyana mahimmancin maganin zazzabin cizon sauro dake da alaka da fasaha.

A fadar kungiyar, kungiyar Mobile Software Solutions ce ta kirkiro wannan wasan halaka zazzabin cizon sauron a karkashin shugabancin Mr Chris Uwaje wanda shine maikujera na masu kirkiro na’urorin komputa na Nijeriya.

Uwaje yace: "ainihin makasudin kirkiro da wannan wasan shine domin a bullo a kuma yi amfani da fasaha wadda zata iya isa ga milyoyin jama’a a ko’ina cikin duniya domin hallaka zazzabin cizon sauro wanda ya tserewa duk fasahar da ake da ita ya zuwa yau. Wani shirin holewa ne dake amfani da kaifin hankali.”

Shugaban sashen koyo ta yanar gizo a Afrika ya goyi bayan wannan wasan; haka kuma Open Media Limited, wata cibiya ta shugabanci a jami’ar Tampere wanda ke Finland, in ji Uwaje.

Uwaje ya bayana cewa wannan wasan ya mayas da hankali ne wajen kawas da zazzabin cizon sauro daga kasar Afrika da kuma duniya baki daya. Uwaje ya kara da cewa Babbar manufar wannan magani shine domin tabbatar da cewa Nijeriya ta sami cimma Makasudan Cin Gaba na majalisar dinkin duniya kana kuma a rage harasar dukiyar da ake yi a Nijeriya da kuma Afrika da kashi 50 cikin 100 kafin shekara ta 2015. Ana fata wanan shirin zai kai ga mutane milyan 50 a Nijeriya, milyan 150 a Afrika ta Yamma da kuma fiye da mutnae milyan 500 a Afrika gaba dayan ta.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG