Accessibility links

Wata Kungiyar Kare Hakin Bil'adama Tana Kalubalantar Katse Hanyoyin Wayar Salula A Najeriya

  • Grace Alheri Abdu

Wata Mace tana waya a gona
Babbar kotun tarayya dake zama a garin Gombe ta fara sauraron karar da gamayyar kungiyoyin ‘yancin dan adam wato Civil Rights Congress ta shigar gabanta, inda kungiyar ke kalubalantar gwamnatin Tarayyar Najeriya da kuma kamfanonin wayar salula a kasar bisa yanke hanyoyin sadarwa a jihohin da gwamnatin tarayya ta kafa dokar- ta-baci.

Bayan sauraron bahasi daga lauyan masu shigar da karar ne alkalin kotun mai shari'a Baba Tunde Kadiri ya shawarci lauyan yayi wadansu ‘yan gyare- gyare a takardar da ya gabatar na shigar da karar.

Bayan zaman sauraron bahasin wakilinmu a shiyar Bauchi Abdulwahab Muhammad ya zanta da lauyan dake wakiltar kungiyar Barrister Luka Musa Haruna.
XS
SM
MD
LG