Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Mace Da Danta Sun Warke Daga Cutar Ebola


Esperance Nabintu da danta

Jiya Talata aka sallami wata majinyaciya da danta a cibiyar jinyar masu fama da cutar Ebola da ke gabashin Congo, bayan sun shafe kwanaki 29 su na ta kokarin ceto rayukansu.

“Ina jin dadi sosai kuma ‘dana lafiyarsa lau,” abin da Espaerance Nabintu ta fada kenan cikin murmushi ga wasu mutane da suka taru a wajen cibiyar domin murnar sallamarta kenan.

Ta share hawaye daga kumatun ‘danta ‘dan shekara guda da haihuwa, Ebenezer Fataki, wanda yake kuka.Ta saka wata riga da aka yi rubutu cikin harshen Faransanci dake cewa “Na warke daga Ebola”


Nabintu da ‘danta duk sun warke daga cutar Ebola, cutar da ta kashe mijin Nabintu ‘yan makonni da suka gabata, a cewar likitoci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG