Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Masarauta A Ghana Ta Haramta Ma Wani Gidan Rediyo Halartar Bikin Gargajiya


Shugaban Ghana Nana Akufo
Shugaban Ghana Nana Akufo

Masarautar gargajiyar al’ummar Ada da ke Accra, babban birnin kasar Ghana ta haramta ma wani gidan rediyo, Radio Ada, halartar bikin gargajiyar yankin, saboda kalaman baci ga sarakunan al’ummar daga wasu ma’aikatan gidan rediyon.

ACCRA, GHANA - Kungiyar ‘yan jarida ta Ghana (GJA) da kungiyar Gidauniyar Kafafen yada labarai ta Afrika ta yamma (MFWA) sun bayyana matakin da masarautar Ada ta dauka a matsayin take hakkin ‘yancin ‘yan jarida da kuma hana al’ummar Ada hakkin samun labarai.

Shugabannin gidan rediyon Ada sun ga babu sunan gidan rediyon a cikin jerin kafofin yada labarai da aka gayyata don bikin gargajiyar Asafotufiami karo na 85, a tashar rediyo na yada bikin gargajiyar tun fiye da shekaru ashirin da suka wuce.

Da suka nemi sanin dalili sai majalisar ta rubuta wa rediyo Ada wasika da sa hannun shugaban shirya bukin cewa, ba su yarda tashar ta kafa tanti a wajen bikin ba; sarakunan gargajiya ba za su yi intabiyu da tashar ba; kuma kada a ga wasu ‘yan jarida uku da suke shiri a wannan gidan rediyo a wajen bukin.

Daga cikin dalilan da masauratar ta bayar shi ne cewa, suna kiran sunayen sarakuna ba da lakabin sarautarsu ba; kuma suna ingiza al’umma da su yi bore ga sarakunan.

Matakin da masarautar ta dauka bai yi wa kungiyar ‘yan Jarida ta Ghana (GJA) dadi ba. Bayan ta tura wakilai su binciki lamarin sai ta shirya taron manema labarai.

Shugaban kungiyar Albert Dwumfour ya ce GJA ta yi imanin cewa takunkumin da aka sa wa gidan rediyon da masu kawo rahoto bai dace ba. Hasali ma, tauye hakkin ‘yancin ‘yan jarida ne kamar yadda sashe na 21 (1) (a) da (f) na kundin tsarin mulkin kasar Ghana na shekarar 1992 da kuma sashe na 19 na yarjejeniyar kasa da kasa kan ‘yancin dan Adam su ka tanada.

Mr. Dwumfour ya kara da cewa, cikin girmamawa, Majalisar Gargajiya ta Ada ba ta da hurumin sanya irin wannan takunkumi ga Rediyon Ada da ma’aikatanta, kuma za ta sa ran ‘yan jarida guda uku da ta bayyana sunansu a cikin wasikarsu.

A wata hira ta musamman da kafar labarai ta Joy dake yada shirye-shiryenta daga Accra ta yi da shugaban kungiyar Gidauniyar ‘yan jarida ta Afrika ta Yamma (MFWA), Suleiman Braimah ya ce tabbas lamari ne na take hakkin ‘yan jarida, ba wai haka kawai ba, har ma da tauye hakkin al’ummar Ada na ‘yancin samun labarai.

Sai dai Sarki Lamido Jibril Sissy, tsohon dan jarida ne kuma basarake ne, ya nuna cewa, duk da yake akwai ‘yancin fadar albarkacin baki, haka kuma ya kamata a dubi hakkin gargajiya, kada manema labarai su dinga wuce gona da iri.

Abdallah Sham’un Bako, shi ma dan jarida ne kuma a nasa bangaren ya nuna cewa, matakin da masauratar ta dauka bai dace ba domin tashar rediyon Ada ta fi kusa da su, kafin wata tasha ta yada al’amuransu lallai wannan tashar ce farko domin haka a duba a sasanta lamarin.

Game da kiyaye rayuwar 'yan jarida ukun da masarautar ta ambaci sunansu, shugaban kungiyar 'yan Jarida na Ghana ya bayyana cewa an tattauna hakan da shugabannin hukumar 'yan sandan Ghana domin ba su kariya yadda za su samu damar gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Saurari rahoton Idris Abdullah:

Wata Masarauta A Ghana Ta Haramtawa Wani Gidan Rediyo Halartar Bikin Gargajiya.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

XS
SM
MD
LG