Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Motar Makaranta da Tayi Hadari A Jihar Tennessee Nan Amurka Ta Kashe Yara Biyar


Masu aikin ceto a wurin hadarin motar jiya Litinin
Masu aikin ceto a wurin hadarin motar jiya Litinin

Wani mummunan hadarin motar daukan yaran makaranta tayi a kusa da birnin Chattanooga dake jihar Tennessee ya jefa iyaye cikinjuyayi

Iyaye dama na nan Amurka na cikin juyayin bayan wani kazamin hatsarin motar daukar ‘yan makaranta da ya abku jiya Litinin inda kuma yara kanana guda shidda suka rasa rayukkansu a birnin Chattanooga dake jihar Tennessee.

‘Yansanda sunce yara kanana kamar 35 ‘yan aji biyar na makarantar firamare ne suke kan motar safar lokacinda ta fadi, kuma ta juya.

Jami’an yankin na Chattanooga sunce yara 23 aka dauka zuwa assibitoci daban-daban dake garin.

Motar 'yan makaranta da tayi hadari a jihar Tennessee
Motar 'yan makaranta da tayi hadari a jihar Tennessee

Haka shima Atone-janar na yankin Hamilton inda abin ya faru, Neal Pinkston ya gayawa kafofin watsa labarai cewa biyar daga cikin yaran a nan take suka rasu a inda aka yi hatsarin, na biyar din kuma ya cika a wata assibitin da aka kai shi.

XS
SM
MD
LG