Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Mummunar Wutar Daji Ta Kashe Mutane 62 A Kasar Portugal


Firefighters run at the scene of a fire which broke out at the headquarters of the Nigeria Football Federation in Abuja, August 20, 2014.
Firefighters run at the scene of a fire which broke out at the headquarters of the Nigeria Football Federation in Abuja, August 20, 2014.

Wata mummunar wutar daji dake ci gadan-gadan ta kashe mutane akalla 62, da yawansu cikin motocinsu a yankin tsakiyar kasar Portugal. An bada rahoton cewa wasu mutanen su akalla 59 sun samu raunuka a lokacin wannan wutar daji da ta tashi a tsakiyar wani zafi mai tsanani tare da hadirin da aka yi, amma babu ruwan sama.

Firayim minister Antonio Costa ya ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku a fadin kasar daga yhau lahadi.

Firayim ministan yace wannan gobarar daji it ace irinta mafi muni da Portugal ta gani cikin ‘yan shekarun nan, kuma yanzu abu mafi muhimmanci shine a ceto rayukan mutanen da ka iya shiga hatsari daga wannan wuta.

Jami’ai sun ce an tura daruruwan ‘yan kwana kwana domin suyi kokarin kasha wannan wuta a yankin Pedrogao Grande mai duwatsu da tsaunuka, kimanin kilomita 150 a arewa maso gabas da Lisbon, babban birnin kasar.

Kasashen Faransa da Spain sun tura jiragen saman kasha gobara domin su taimaka wajen yaki da wutar. Ita ma Kungiyar Tarayyar Turai tana shirin kaddamar da wani kyamfen din bayar da agajin gaggawa.

Sakataren harkokin cikin gidan Portugal, Jorge Gomes, yace wutar ta yadu da saurin gaske, kuma zai yi wuya a tantance ko mutanen da ta kona cikin motocinsu suna kokarin gudu ne ko kuma ta rutsa da su ne haka kwatsam.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG