Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Sabuwar Cuta Na Lalata Gonaki a Jihar Filato


FILE -Wata mata a gonarta Nov. 11, 2009.
FILE -Wata mata a gonarta Nov. 11, 2009.

Fannin noman albarkatun gonaki a Jihar Filato dake tsakiyar Najeriya, na fuskantar kalubale bayan da aka gano wata cuta dake barnata amfanin gona. Filato, jiha ce da ta yi fice a fannin noman kayan marmari da ma hatsi.

Wata sabuwar cutar tsiro da manoma suka kasa tantance ta, ta na lalata gonaki masu yawan gaske a jihar Plateau dake arewa maso tsakiyar Najeriya.

A cewar manoman, lamarin ya janyo masu hasara mai yawa, ganin irin barna da wannan cutar ke yi wa itatuwa kamar na gwaiba, mangwaro da sauran itatuwa a karamar hukumar Qua'an pan a jihar Plateau.

Manoman sun yi kira ga hukumomi da su kawo masu dauki don kawo karshen wannan sabuwar cuta da ke ci gaba da addabar gonakin nasu.

Shugaban sashen kula da lafiyar dabbobi a cibiyar binciken lafiyar dabbobi ta kasa dake Vom a jihar Plateau Farfesa Garba Hamidu Sharubutu, ya na cikin wadanda wannan sabuwar cutar ta addabi gonakinsu kuma ya yi wa wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka, Zainab Bababji bayanin barnar da wannan cutar ta yi wa gonarsa.

Wani mai shari’a Thomas Naron da gonarsa ta kamu da wannan cutar, shi ma ya yi kira ga hukumomi da su kawo daukin gaggawa domin ceto gonakinsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG