Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Tankar Man Fetur Ta Iran Ta Kama Wuta A Teku


Tankar da ta kama wuta akan teku
Tankar da ta kama wuta akan teku

Wata tankar kasar Iran dauke da danyen man fetur akan hanyarta zuwa kasar Koriya ta kudu ta yi taho mugama da wani jirgin ruwan kasar Sin, dake dauke da hatsi daga Amurka zuwa Sin.

Wata tankar man fetur ta Iran ta kama wuta bayan da ta kara da jirgin ruwa dake dauke da kayan kasar Sin a ranar Asabar a kan iyakar gabashin kasar Sin, yau Litinin kafar yadda labarai ( CCTV) ta kasar Sin ta ce jirgin na fuskantar hadarin fashewa da kuma nitsewa cikin ruwa. Bayanai na nuna cewa jami'ai da masana na cikin masu ceto mutane.

'Yan Iran 30 ne suke cikin cikin ma'aikatan tankar da mutane biyu yan asalin Bangladesh ne suka bace tun da aka yi hatsarin ranar Asabar din da ta wuce, duk da cewa, kafofin yadda labarai sun bayar da rahoton cewa an gano gawar daya a yau Litinin.

Tankar tana tafiya akan ruwa daga Iran zuwa Koriya ta Kudu inda ta yi taho mu gama da jirgin ruwa mai suna CF Crystal wanda yake da tazarar kilomita 257 da tekun Shanghai.

An ceto mutane 21 dukansu ‘yan kasar Sin, kuma jirgin ruwan na dauke da hatsi daga Amurka zuwa kasar Sin din.

Sakamakon hadarin ya janyo tankar da ke dauke da man fetur mai nauyin tan136,000 ya fashe ya kuma kama wuta.

China, Koriya ta Kudu da Amurka sun aika da jiragen ruwa da jiragen sama don taimakawa wajen binciko waddanda suka bace

Har yanzu ba'a kiyasta addadin man fetur din da ya zube ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG