Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Watakila Nan Da Gobe Asabar Ramin Da Ake Hakawa Zai Kai Ga Mahaka Ma'aidinai A Chile


Ministan hakar ma’adinai na kasar Chile, Laurence Golborne, yace da zarar ramin ceto mutanen ya kai ga inda suke, ana iya daukar tsawon kwanaki 10 kafin a fito da su baki daya zuwa kan doron kasa.

Jami’ai a kasar Chile sun ce watakila nan da gobe asabar ramin nan da ake hakawa domin ceto ma’aikatan hakar ma’adinai su 33 dake karkashin kasa zai kai ga inda suke.

Ministan hakar ma’adinai na kasar Chile, Laurence Golborne, yace da zarar ramin ceto mutanen ya kai ga inda suke, ana iya daukar tsawon kwanaki 10 kafin a fito da su baki daya zuwa kan doron kasa. Golborne yace kwararru zasu nazarci kasa da duwatsun dake kewayen ramin da aka tona din domin tantance ko za a bukaci daure bakinsa da karfe domin tabbatar da cewa bai rusa ba.

Yau watanni biyu da ‘yan kwanaki ke nan wadannan ma’aikata su 33 su na wani wuri mai zurfin mita 600 a karkashin kasa, bayan da bakin ramin da suka shiga don hakar jan karfe ya rusa ya rutsa da su. Ana tura musu abinci da ruwan sha da wasiku da wasu kayayyakin bukatu ta wani karamin ramin da aka tona zuwa inda suke.

Likitoci da kwararrun ma’aikatan ceto su 16 su na shirye-shiryen zakulo mahaka ma’adinan zuwa kan doron kasa. Hukumomi sun ce za a zura wasu daga cikin ma’aikatan ceto da likitocin zuwa inda mahakan suke domin kara karfafa musu guiwa.

XS
SM
MD
LG