Accessibility links

Yau aka fara Azumin watan Ramadan a Najeriya.

Yau aka fara Azumin watan Ramadan a Najeriya, koda yake sanarwar yazo a makare bayan da wasu kafofin yada labarai suka bayana sanawar da babban sakataren majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya Farfesa, Ishaq Oloyede ya bayar cewa za’a soma Azumin ne a ranar lahadi.

Bayan haka sai aka samu wani sanarwar wace shugaban kwamitin bada shawarwari akan lamurin addini Musulunci na fadan mai martaba Sarkin Musulmi,Farfesa, Sambo Waleed Junaidu, ya gabatar a fadar ta mai martaba Sarkin Musulmi a sokoto.

Sanarwar ya biyo bayan wani taro mai tsawo da ‘yan kwamitin wanda ya kunshi manyan shehunnan Malamai da suka gudanar tare da Sarkin na Musulmi.

Farfesa, Junaidu yace an samu wasu rahotanin ganin watan na Ramadan ne daga baya, wanda yace kuma ya zama wajibi a tantance.

XS
SM
MD
LG