Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Watsa Takardun Naira Ya Jefa Wata Mata 'Yar Gombe Hannun Hukumar EFCC


EFCC
EFCC

A cewar kakakin Hukumar EFCC, Dele Oyewale, an ga Janty Emmanuel tana watsa kudin a wurin taro na G-Connect dake shiyar Tumfure ta jihar Gombe, a ranar Litinin 20 ga watan Mayun da muke ciki.

A wani yunkurin gaggawa na yakar dabi'ar wulakanta kudi, Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin najeriya zagon kasa ta kama wata mata 'yar Gombe mai suna Janty Emmanuel saboda watsa takardun Naira dubu-dubu a bainar jama'a a yayin wani biki.

A cewar kakakin Hukumar EFCC, Dele Oyewale, an ga Janty Emmanuel tana watsa kudin a wurin taro na G-Connect dake shiyar Tumfure ta jihar Gombe, a ranar Litinin 20 ga watan Mayun da muke ciki.

Janty Emmanuel wanda ake tuhuma da laifin wulakanta takardun Naira
Janty Emmanuel wanda ake tuhuma da laifin wulakanta takardun Naira

Nan da nan al'amarin wanda aka nada a faifan bidiyo ya karade shafukan sada zumunta abinda ya ja hankalin Hukumar EFCC.

Ta hanyar yin amfani da bayyanan sirrin, ba tare da bata lokaci ba Hukumar EFCC ta cafke Janty Emmanuel domin amsa tambayoyi.

A yayin amsa tambayoyin ne ta amsa aikata laifin.

Hukumar ta sha alwashin cigaba da yakin da take yi da wulakanta kudi, laifin da dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta tanadi hukunci akansa.

Hukumar EFCC tayi gargadin cewar ba zata lamunci wannan dabi'ar ba kasancewar tana kaskantar da kimar takardar kudin naira.

Janty Emmanuel zata fuskanci tuhuma a kotu da zarar an kammala bincike akan lamarin, kuma idan an sameta da laifi, zata fuskanci hukuncin tara ko dauri ko a hada mata duka biyun.

Al'amarin na zuwa ne biyo bayan shari'ar dan daudun nan, Idris Okuneye da aka fi sani da "Bobrisky", da aka aika gidan gyaran hali tsawon watani 6 saboda aikata makamancin wannan laifi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG