WASHINGTON, D.C —
Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce hukumar ta dauki matakin da ya kamata ta dauka cikin gaggawa kan yaki da cutar coronavirus.
Ya fadi hakan ne a matsayin martani kan sukar da hukumar ke fuskanta, musamman daga kasar Amurka, wacce ke daga cikin masu bai wa WHO tallafi.
Amurka ta kuma kasance kan gaba a duk fadin duniya wajen yawan masu dauke da cutar, da kuma adadin wadanda suka rasa rayukansu.
A yayin Wata tattaunawa da yayi da manema labarai a kasar Geneva, Tedros ya ce "tun daga farko, WHO ta dauki matakan da suka kamata wajen yi wa Duniya gargadi."
Za ku iya son wannan ma
-
Afrilu 30, 2022
An Ware 20-30 a Matsayin Satin Rigakafi Na Duniya
-
Afrilu 24, 2022
Kudin Kujerar Zuwa Hajji Zai Karu Zuwa Naira Miliyan 2.5
Facebook Forum