Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WHO Ta Gargadi Kasashen Da Ke Yunkurin Dage Dokar Zirga-zirga


Shugaban hukumar WHO Tedros Ghebreyesus
Shugaban hukumar WHO Tedros Ghebreyesus

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta gargadi kasashen da suka zaku su dage dokar hana zirga-zirga domin dakile bazuwar cutar COVID-19 da su yi taka-tsantsan.

Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Juma’a, Shugaban WHO, Dr. Tedros Ghebereyesus ya ce su ma suna so al’amura su dawo kamar da, amma idan ba a yi taka-tsantsan ba, “al’amuran ka iya rincabewa.”

Shugabannin kasashen duniya ciki har da na Amurka, sun kintayi karshen makon nan da za a yi bukukuwan Easter a matsayin lokacin da za a dage dokar hana zirga-zirga.

Amma da yawa daga cikin kasashen sun janye inda suka tsawaita har sai zuwa karshen watan nan.

Ghebereyesus ya kara da cewa, WHO na aiki tare da kasashen da al’amarin ya shafa kan yadda za a janye dokar a hankali.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG