Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WHO Ta Yi Kashedi Ga Kasashen Afrika Game Da Sassauta Dokokin Kulle


Hukumar kiwon lafiya ta WHO ta yi kashedi ga kasashen Afrika a jiya Alhamis game da sassauta dokokin kulle, yayin da kamuwa da cutar ke kara ta’azzara a nahiyar a cikin watan da ya gabata.

Darektan WHO a yankin Afrika, Matshidiso Moeti ta fada a wani taron manema labarai ta bidiyo, yana mai cewa, muna matukar damuwa game da yawan masu kamuwa da cutar kamar yanda muke gani a wasu kasashe, inda aka yi gaggawar dage dokokin hana zirga zirga.

Ta ce, sama da kasashen Afrika 20 ne suka samu sabbin kamuwa da cutar fiye da wasu, makwanni a baya, inda kasar Afrika ta Kudu tafi kowa yawan masu kamuwa, amma kuma an samu karuwan cutar a Kenya da Madagascar da Najeriya da kuma Zimbabwe.

Moeti ta ce, kasashen Uganda da Seychelles da Mauritius sun taka rawar gani wurin dakile cutar.

WHO ta ce, an tabbatar da mutum dubu dari takwas sun kamu da cutar a Afrika kana wasu dubu 18 kuma sun mutu da cutar.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG