Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WHO, Tayi Kashedi Akan Amfani Da Dabaru Na Daban A Yaki Da Coronavirus


Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, jan hankali game da ikirarı da Kasashe da dama ke yi na cewa sun gano hanyoyi da magunguna na dakile cutar COVID -19 wanda ba wanda hukumar lafiya ta duniya ce a amince da su ba.

Shugaban hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO, yayi kashedi a kan dabarun amfani da wata hanya daban a yaki da cutar coronavirus cewa bai dace ba.

A wurin wani taron manema labarai a Geneva a jiya Litinin, babban darektan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, yace jami’an kiwon lafiya su maida hankali wurin amfani da maganin rigakafi kadai amma ba wata hanyar da zata jefa jama’a cikin hadarin kamuwa da cutar.

Hanyar yaki da cutar a kaikaice, ana amfani da ita ne a lokacin da galibin jama’a suke da kariya daga cuta saboda an kai ga cimma babbar kariya tsakanin jama’a.

Ba a taba amfani da yaki da cuta a kaikaice a matsayin dabarun yaki da barkewar annoba ba a tarihin kiwon lafiyar jama’a. Hanya ce mara inganci a kimiyance da kuma bisa tsarin yaki da cuta mai yaduwa inji Tedros.

WHO tayi kiyasi cewa kimanin kashi goma cikin dari a duniya sun kamu da coronavirus. Har iyau ba a san adadin mutanen da suke bukata wannan hanya ta yaki da cutar a kaikaice.

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG