Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WHO Za Ta Yi Bincike Kan Yanayin Ayyukanta Yayin COVID-19


Tambarin hukumar WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa za ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa wanda zai yi bincike kan yanayin kokarinta na shawo kan COVID-19, da kuma irin matakan da su kuma gwamnatoci a duk fadin duniya suka dauka.

Hakan na faruwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi matukar sukar hukumar, inda ya zarge ta da zama 'yar koren China.

A ranar Talata ne ma Amurkar ta bayyana cewa za ta fice daga WHO a cikin tsawon shekara daya.

Tsohuwar frai ministar New Zealand, Helen Clark da tsohon shugaban Liberia, Ellen Johnson Sirleaf sun amince su jagoranci kwamitin, a cewar darakta janar na WHO.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG