Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana'izar Winnie Mandela


Akwatin gawar Winnie Mandela lullube da tutar Afirka ta Kudu
Akwatin gawar Winnie Mandela lullube da tutar Afirka ta Kudu

An yi jana'izar Winnie Mandela, tsohuwar matar Nelson Mandela, wacce ta rasu a farkon watannan tana mai shekaru 81.

Yau Asabar aka yi jana’izar, marigayiya Winnie Mandela, tsohuwar matar marigayi tsohon shugaban Afrika ta Kudu, Nelson Mandela, wacce ta kasance daya daga cikin fitattun mutanen da suka yaki mulkin wariyar launin fata a kasar.

Mutum kusan dubu 40 ne suka taru a babban fili wasan kwallon kafa na Orlando da ke Soweto a Birnin Johannesburg, domin yin ba-kwana.

Yayin jawabinsa, shugaban kasar, Cyril Ramaphosa ya kwatanta Winnie a matsayin “mata mai magana da babbar murya, ba tare da ta nuna tana tsoron kowa ba.”

A wajen taron ban-kwanan, diyar marigayiya Winnie, wato Zenani, ta bi sahun mahaifiyarta wajen fadin gaskiya ba tare da tsoro ba, inda ta yi hannunka mai sanda, ta kira wasu masu yabon mahaifaiyarta bayan da ta rasu a matsayin “munafukai,” kamar yadda ta ce.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG