Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wutar Dajin California: Har Yanzu Ana Kwashe Jama'ar Da Ta Dosa


Wutar dajin Kalifoniya dinnan mai lakabin "Thomas."
Wutar dajin Kalifoniya dinnan mai lakabin "Thomas."

Wutar nan mai kama da ta bala'i da ke ta lakume wurare a jahar California ta Amurka, ta sa an kwashe mutane sama da dubu 88, kuma har yanzu ana ta kwasar jama'a don a ceci rayukansu.

An bayar da wani sabon umurnin kwashe mutane a karamar hukumar Santa Barbara da ke Kudancin jahar California da safiyar jiya Lahadi.

Hakan na faruwa ne yayin da wutar daji mafi girma da jihar ta taba gani ke barazana ga garuruwa da dama da ke bakin gaba.

An umurci mazauna yankunan Carpinteria da Montecito da su tashi tun da safiyar jiya Lahadi.

Gargadin na zuwa ne yayin da wutar da ake wa lakabi da “Thomas” ke dada bazuwa zuwa birnin Santa Barbara, mai tazarar kilomita 160 yamma da birnin Los Angeles.

Mutane kimanin 88,000 aka kwashe zuwa yanzu saboda barazanar ta wutar “Thomas,” wadda hukumar kashe gobarar jahar ta ce ta sha kanta da kashi 15% ya zuwa daren ranar Asabar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG