Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wutar Dajin California Ta Karu Sosai


Wani jirgin sama na aikin kashe wuta
Wani jirgin sama na aikin kashe wuta

Shu'umar wutar dajin nan ta California, wadda ake zargin wani mutun da kunna ta da gangan, ta fadada da kilomita 85 murabba'i.

Wata wutar daji a kudancin California wadda ta fara tashi ranar Litini da ta gabata, zuwa jiya Asabar ta karu zuwa kilomita 85 murabba’i, yayin da ‘yan kwana-kwana ke ta kokarin hana wutar lakume gidajen mutane a yankin Holy Jim Canyon.

Jiragen sama na kashe wuta sun yi ta watsa sinadarin hana wuta ci akan gidaje, a sassan Lake Elsinore da sauran wuraren da ke kusa da Gandun Kurmin Cleveland na Kasa, a yayin da aka baiwa mutane wajen 20,000 umurnin barin gidajensu.

Ana tuhumar wani mutum dan shekaru 51 da haihuwa mai suna Forrest Clark da tayar da wutar, wacce ake wa lakabi da Holy Fire (wato Wuta Mai Tsarki) kuma ya gurfana gaban kotu ranar Jumma’a, to amma sai aka dage sauraron karar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG