Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wutar Rikici Ta Soma Ruruwa A Jam'iyyar APC


APC

Sanata Ahmed Tinubu shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar APC ya rubuta budaddiyar wasika wa shugaban jam'iyyar Chief Oyegun inda ya bukasheshi da ya sauka daga kan mukaminsa na shugabancin jam'iyyar bisa zargin wasu halaye da yace sun sabawa tsarin dimokradiya

A wasikar da Sanata Ahmed Tinubu ya rubuta ya zargi Chief Oyegun da wasu halaye da yace sun sabawa shirin dimokradiya da kuma turbar da jam'iyyar APC ta kafu akai.

Bola Tinubu ya zargi Chief Oyegun da mika sunan Rotimi Akinrindolu ga hukumar zaben kasar INEC sabanin shawarar kwamitin sauraren korafe korafen zaben fidda gwamni wanda ya bukaci a sake sabon zabe saboda zargin an tafka magudi a zaben fidda gwani da aka gudanar.

Tuni wasu masu lura da harkokin siyasa ke kwatanta rikicin da na jam'iyyar adawa ta PDP.

Alhaji Abubakar Na Baban Yawo wani dan jam'iyyar APC yace a ganinsa maganar Tinubu gaskiya ce. Inji shi Chief Oyegun yana yiwa jam'iyyar zagon kasa. Ta dalilin haka ya kira Shugaba Buhari ya sanya wandunan soja da na farar hula domin, wai akwai maciji a karkashin kujera.

Amma masana kan harkokin siyasar kasar irinsu Dr Umar Kyari na jami'ar Abuja na ganin rikicin ba sabon abu ba ne kuma dole ta bi a hankali..Yace an dade anaharsashe ana kuma fada cewa akwai wutar rigima akasa cikin jam'iyyar. Abun da ya jawo haka a cewar Dr Kyari shi ne iya APC hadin gambiza ce.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

XS
SM
MD
LG