Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Amsa Laifin Sacewa Da Daure Mata 3 A Gidansa Na Shekara 10


Ariel Castro tare da lauyoyinsa a cikin wata kotun Cleveland dake Jihar Ohio, jumma'a 26 Yuli, 2013.

Za a yi masa daurin rai da rai, da karin shekaru dubu daya, a gidan kurkuku, bayan da masu gabatar da kara suka ce zasu janye bukatar a yi masa hukumcin kisa

Wani ba Amurke ya amsa laifin da aka tuhume shi da aikatawa na daure wasu mata su uku a gidansa dake birnin Cleveland a Jihar Ohio, har na tsawon shekaru goma, inda ya yarda za a yi masa daurin rai da rai, tare da karin shekaru dubu daya. A saboda amsa laifin da yayi, su kuma masu gabatar da kara sun yarda ba zasu nemi da a yanke masa hukumcin kisa idan an same shi da laifi ba.

Tsohon direban bas na daukar ‘yan makaranta Ariel Castro, wanda aka gani da sabon gemu fari, ya bayyana gaban wata kotu jiya jumma’a a birnin Cleveland cikin kayan fursunoni mai launin lemo. A lokacin ya amsa aikata laifuffuka guda 937 da ake tuhumarsa a kansu, ciki har da daruruwa da suka shafi sace wadannan mata, da daure su da sarka tare da yi musu fyade har sai bayan da daya ta samu kubucewa a cikin watan Mayu kafin ‘yan sanda su kwanto saura biyun.

Castro, mai shekaru 53 da haihuwa, ya kuma amsa laifin kisan kai a wannan lamarin ta hanyar yi ma daya daga cikin matan ciki, sannan ya lakkada mata mummunar duka har sai da ta yi bari. Daya daga cikin matan kuma ta samu cikin yarinya a lokacin da take daure a gidan Castro har ta haifi yarinyar da yanzu shekarunta 6.

Babu daya daga cikin matan su uku wadanda Castro ya sace daga kan titi daga shekarar 2002 zuwa 2004, da ta bayyana a cikin kotun. Kwanakin baya suka yi wani faifan bidiyo su na godewa mutanen birnin Cleveland a saboda goyon bayan da suka ba su a lokacin da suke daure.

Alkalin yace za a bayyana hukumci kan Castro a shari’ance a cikin mako mai zuwa.
XS
SM
MD
LG