Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya kamata gwamnatin Nigeria ta zanta Boko Haram


Wani sojan Nigeria ne e tsaya cikin barnar da harin kunar bakin wake ya yiwa ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Abuja, barna a watan jiya.
Wani sojan Nigeria ne e tsaya cikin barnar da harin kunar bakin wake ya yiwa ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Abuja, barna a watan jiya.

Wani kwamiti da gwamnatin Nigeria ta kafa, yace ya kamata gwamnati ta zanta da yan kungiyar Boko Haram, kungiyar da aka dorawa laifi kai hare hare da dama a cikin Nigeria.

Wani kwamitin da gwamnatin Nigeria ta kafa, yace ya kamata gwamnati ta zanta da yan kungiyar Boko Haram, wata kungiyar wasu Musulmi masu ra'ayin rikau, wadda aka dorawa alhakin kai munanan hare hare, ciki harda wanda aka kai ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake birnin Abuja a watan jiya.

Shugaban kwamitin, Usman Galtimari yace ya kamata gwamnatin Nigeria tayi nazarin yin shawarwari da yan kungiyar Boko Haram bisa sharadin cewa, kungiyar zata yi watsi da yin tarzoma. Yace ya kuma kamata bayan zantawar, a kaddamar da wani shirin sasantawa.

Ita dai kungiyar Boko Haram tana so ne a kaddamar da amfani da shari'ar Musulunci a Nigeria, kasar data fi kowace yawan jama'a a nahiyar Afrika. An dai dora kungiyar laifin kai munanan hare hare da harbe harben da take auna shugabanin a arewa maso gabashin Nigeria, kuma tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai hare haren bama bamai a Abuja.

Rahotan da aka gabatarwa mataimakin shugaban Nigeria, Namadi Sambo, a jiya Litinin ya dorawa laifin kamarin tarzoma akan gwamnati. Rahoton yace gazawar gwamnati ta kawar da fatara da talauci da kuma magance zaman kashe wando a arewacin kasar da kuma wasu kura kurai daga bangarorin jami'an tsaron kasar, sune suka kara ruruta wutar rashin zaman lafiya a yankin.

Haka kuma rahoton ya bada shawarar a kara musayar bayanan da kungiyoyin kasashen waje da kuma karawa yankin arewacin kasar kasafin kudi domin a gyara Masalatai da coci cocin da aka lalata da kuma samar da kafar da shugaban kasa da gwamnoni da kuma shugabanin kanana hukumomi zasu tattauna batutuwan tsaro.

Mataimakin shugaban Nigeria Namadi Sambo, ya lashi takobin kaddamar da shawarwarin da kwamitin ya gabatar a zaman matakin gaggawa.

XS
SM
MD
LG