Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Biyu A Maiduguri


'Yan babur masu Achaba a garin maiduguri a watan Nuwambar 2010.

Wasu 'yan bindigar da 'yan sanda suka ce su na kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ce sun kashe aluya da wani ma'aikacin gwamnatin Borno

‘Yan sanda a yankin arewa maso gabashin najeriya sun ce wasu ‘yan bindigar da ake kyautata zaton ‘ya’yan kungiyar nan ce da aka fi sani da sunan Boko Haram sun kashe wani lauya da wani ma’aikacin hukumar agajin gaggawa ta Jihar Borno.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Borno, Simeone Midenda, ya fada yau alhamsi cewa an kai harin ne cikin daren jiya laraba a garin Maiduguri inda kungiyar ta ke da hedkwatarta a da.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ambaci Midenda yana fadin cewa wasu ‘yan bindiga hudu dauke da bindigogi samfurin Kalashnikov sun kashe mutanen biyu cikin gidajensu.

Babu wanda aka kama dangane da wannan harin.

XS
SM
MD
LG