Wasu daga cikin 'yan jam’iyyar PDP a shiyyar tsakiyar jihar Pilato sun yi kira ga hukumar zabe da ta soke zaben ‘yan majalisun tarayya a yankin. Kamar yadda jami’in tattara kuri’u a yankin ya gabatar, saboda wasu matsaloli da suka gano a rumfunan zabe guda tara a karamar hukumar Kanam.
Hukumar zaben dai ta ayyana cewa jam'iyyar APC ce ta lashe zaben kujerar sanata da na dan majalisa a yankin ba tare da bayyana yadda aka warware matsalolin ba.
A halin da ake ciki dai hukumar zaben zata gudanar da zaben sanata a daukacin shiyyar kudancin jihar ta Pilato, da na dan majalisan Jos ta Arewa da Bassa a majalisar tarayya duk daga bangaren jihar Pilato ta Arewa.
Ga rahoton wakiliyar sashen Hausa na Muryar Amurka Zainab Babaji.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 07, 2023
Ranar Karfafawa Mata Sa Hijabi
-
Fabrairu 07, 2023
An Yi Wa Dimokradiya Karan Tsaye - Kwararrur Siyasa
-
Fabrairu 06, 2023
Har Yanzu Ana Tsaka Mai Wuya Kan Batun Sabbin Kudade A Najeriya
Facebook Forum