Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Kasashen Afirka Su Rage Dogaro Da Kayan Kasashen Waje – Tsohon Shugaban Ghana, Mahama


Tsohon shugaban Ghana, John Dramani Mahama
Tsohon shugaban Ghana, John Dramani Mahama

Ya yi jawabin ne a wajen taron kasuwanci na Afirka karo na 24 da makarantar kasuwanci ta Harvard ta shirya.

Tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama ya bayyana dogaron da kasashen Afirka take yi kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje a matsayin abin kunya.

Ya yi jawabi ne a wajen taron kasuwanci na Afirka karo na 24 da makarantar kasuwanci ta Harvard ta shirya.

“Dole ne mu matsa kaimi don dogaro da kai kan muhimman kayayyaki irin su shinkafa, tumatur, albasa, da man da kayan lambu, da dai sauransu.” Tsohon shugaba Mahama ya ce.

Shugaban kampanin shige da fice a Ghana Abdallah Tsoho Salga ya c Lamari ne da ya jima yake ci musu tuwo a kwarya.

A cewar shi, ana sayar wa kasashen waje albarkatun Afirka sai kuma dan Afirka ya hau jirgin sama kuma ya tafi ya siyo kayan kuma ya dawo da su nahiyar.

Mallam Jafaru Dankwabia, mataimakin daraktan binciken yanayi da kare martaban abinci, ya ce ya kamata a baiwa masu binciken Abinci damar binciko abincin da zai yi auki da kuma kula da manoma.

Ya kara da cewa, manoma kashi 80% ba su da ilimi, kashi 80% kuma tsofaffi ne, yana mai jaddada cewa, ya kamata matasa su saka kansu cikin aikin noma, kuma yanzu ana amfani da na’u’rorin zamani wajen yin noma a duniya.

XS
SM
MD
LG