Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya kamata Mawaki Davido Yayi Taron Wake-wake Kyauta Ga Masoyansa - Tinubu


Seyi Tinubu
Seyi Tinubu

Sanannen dan kasuwa Seyi Tinubu, dan Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a Najeriya ya bukaci shahararren mawakin Najeriya Davido ya yi taron wake-wake da raye-raye kyauta ga masoyansa don ya yi musu godiya.

Tinubu yayi wannan kiran ne saboda kudaden da abokan arziki da masoya suka tara wa mawakin. Davido dai ya yi kira ga abokansa da kowannensu ya ba shi miliyan 1. Mutane da yawa sun tura mashi kudin wanda suka kai sama da naira miliyan 160.

A halin da ake ciki kuma, hamshakin dan kasuwa Obi Obinna Iyiegbu, wanda aka fi sani da Obi Cubana, ya taya mawakan PSquare murnanar zagayowar ranar haihuwarsu bayan da suka sasanta tsakaninsu.

Wannna na zuwa ne bayan da aka ga shahararrun mawakan a bidiyo suna rungumar juna bayan sun kwashe shekaru da yawa basa ga maciji.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG