Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken Ya Isa Najeriya


Antony Blinken, Sakataren Harakokin Wajen Amurka
Antony Blinken, Sakataren Harakokin Wajen Amurka

A cigaba da ziyarar Afurka da ya ke yi, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya isa Najeriya, inda zai dada bayyana manufofin Amurka game da Afurka.

Kafafen yada labarai a Najeriya sun bayyana cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya isa Najeriya, inda zai yi wani mashahurin jawabi kan manufofin gwamnatin Biden game da Afurka a yau dinnan Alhamis a ziyarar kasashe uku da ya ke yi a nahiyar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce Blinken zai tattauna da takwaran aikinsa, Ministan Harkokin Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, da Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Mataimakin Shugaba Yemi Osinbajo, bayan isarsa Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Cikin batutuwan tattaunawar akwai na kare lafiyar jama’a a duniya, fadada hanyar samun makamashi da bunkasar tattalin arziki, da kuma karfafa tsarin dimokaradiyya.

Dimokaradiyya ce babban maudu’in Blinken a inda ya fara yada zango jiya Laraba, wato kasar Kenya, inda ya gaya ma wani gungun ‘yan gwagwarmayar kare ‘yancin dan adam cewa jiya Larabar a birnin Nairobi cewa duniya na fama da abin da ya kira, “koma baya” a tsarin dimokaradiyya. Ya yi gargadin cewa “hatta Kenya mai ingantaccen tsarin dimokaradiyya” ta yi ta fama da karuwar labaran karya, matsalar cin hanci da rashawa, tashin hankali mai nasaba da siyasa da kuma tsangwamar masu kada kuri’a.

XS
SM
MD
LG