Kungiyar Liverpool da Manchester City za su kece raini a ranar Lahadi a ci gaba da cin kofin gasar Premier ta Ingila.
Wadannan kungiyoyi na daga cikin zakarun gasar, inda yanzu haka Liverpool ke rike da kofin gasar.
City wacce ita ma ta sha daukan kofin, kuma yanzu haka ma tana gaban Liverpool din da maki bakwai, ta buga wasannin 13 cikin gasa daban-daban da ake bugawa a kasar ta Ingila, ba tare da ta sha kaye ba.
Idan Liverpool ta samu nasarar wannan wasa, hakan zai kara ta da kaimin ‘yan wasan kungiyar yayin da city ke kokarin ganin wannan wasa ya zama mata na 14 da take samun nasara a jere.
Idan kuma ‘yan wasan na Jurgen Klopp suka maku, hakan zai kara fadada gibin makin da aka bata zuwa maki 10 tsakaninta da saman teburin gasar.
Ita dai City ana mata kallon kungiyar da babu wanda ya kai ta iya kai hari a gasar Premier yayin da ita kuma Liverpool ta kware wajen tsaron gida.z
Za a buga wasan ne a filin Liverpool na Anfield.
Dubi ra’ayoyi
Ko ka yi rijista da mu? Shiga shafinka
Ba ka yi rijista da mu ba? Yi rijista
Load more comments