Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Tabbata An Yi Amfani Da Guba A Syria


Yarinya a Syria
Yarinya a Syria

Kungiyar dake yaki da makamai masu guba ta fada a yau Laraba cewa, wani bincike da ta gudanar ya tabbatar akwai yiwuwar amfani da gubar Chlorine a harin da aka kai a arewacin Syria a cikin watan Faburairu

Kungiyar ta fitar da rahotonta ne a kan tambayoyi da ta yiwa ma'ikatan kiwon lafiya da wadanda suka shedi al'amarin tare da gudanar da wasu gwaje gwaje a inda aka kai harin a yankin Saraqeb dake gundumar Idilib


A wannan lokaci, kungiyoyin kiwon lafiya da wadanda suka fara bada bahasi, sun ce fararen hula sun nuna alamar sun shaki iskar Chlorine, suna fama da rashin nunfashi kuma ana jin warin Chlorine a cikin tafafinsu


Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta zargi rundunar shugaban Syria Bashar al-Assad da kai wannan harin guba a kan yankin da yan tawaye suke.


Kungiyar yaki da makamai masu gubar tace aikinta ne ta binciko ko yalla an yi amfani da makamai masu amma bata da alhakinta gano wanda ya kai harin.


Gwamnatin Syria ta sha musunta amfani da makamai masu guba a cikin yakin kasar da aka fara tun cikin watan Maris shekarar 2011.

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG