Accessibility links

Ya Yiwu Koriya Ta Arewa Sake Gwajin Makamin Mai Linzami Mako Mai Zuwa

  • Grace Alheri Abdu

Makamai masu linzami na Koriya Ta arewa a wani bukin fareta
Wani babban jami’in tsaron KTK ya bayyana yau Lahadi cewa mai yiwuwa ne KTA tana shirin yin wani gwajin makami mai linzami ko kuma wata takala cikin wannan makon tare da gargadin da tayi cewa, ba zata iya bada tabbacin kare lafiyar jami’an diplomasiya dake Pyongyang ba.

Jim Jang-Saoo, babban mai ba shugaban kasa Park Geun-Hye shawarwari kan harkokin tsaron kasa ya bayyana cewa, za a yi gwajin makamin ko takalar ne bayan ranar laraba, ranar da KTA tace jami’an diplomasiya su fice daga Pyongyang.

Yace ainihin burin KTA shine tilastawa Washington da Seoul bata sassaucin diplomasiya, sai dai ya kara da cewa, KTK tana kan bakanta cewa, rundunar sojanta tana zaman ko ta kwana ko da kuwa barazana ce kawai Pyongyang ke yi.

Yau ne kuma babban jami’in sojojin Koriya Ta Kudu ya janye wani zama a Washington da shugaban hafsoshin Amurka sabili da damuwar da kasar ke da ita da Kotiya Ta Arewa.

Dama babban hafsan sojojin Amurka janar Martin zai gana da takwaransa na Seuol Janar Seung-jo a wajen wani taron kwamitin soja da ake gudanarwa shekara shekara da za a yi ranar 16 ga wannan watan. Sai dai kakakin hafsan hafsoshin KTK ya bayyana yau Lahadi cewa, Seoul ta damu cewa, Pyongyang tana iya daukar wani matakin soja na takala a bayan Janar Jung.
XS
SM
MD
LG