Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani zama a jiya Alhamis don tattaunawa kan batun harin soja da kasar Turkiyya take kai wa a arewa maso gabashin Syria, wanda ta kwatanta shi a matsayin "tsararre kuma wanda ya dace" a yakin da take yi da ta’addanci.
Harin na faruwa ne a daidai lokacin da mayakan Kurdawa a yankin, suke kiran neman dauki “don su kare mutanensu daga” abin da suka kira “kisan kiyashi.”
Jami'an diplomasiyya a kwamitin sun yi magana da baki daya kan wannan kutse da Turkiyyan ta yi, wanda suka ce zai kara jefa al’umar yankin cikin halin ha’ula’i, kuma har wasu mambobin kwamitin sun yi kira ga Turkiyyar kai tsaye, da ta kawo karshen wannan farmaki.
"Muna kira ga Turkiyya da ta kawo karshen wannan matakin soji da ta dauka ita kadai, saboda mun yi imanin cewa, ba zai magance matsalolin rashin tsaro da Turkiyya ke fuskanta ba," Inji Mataimakin jakadan Jamus da ke kwamitin, Jurgen Schulz, wanda ya yi magana a madadin mambobin Kwamitin Tsaron na nahiyar Turai su biyar, ciki har da Estonia, wacce a shekarar 2020 za ta zama mamba a kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya.
Turkiyya ta kaddamar da hare-haren saman ne a ranar Larabar da ta gabata, sannan daga baya sojojinta suka kutsa kai cikin kasar ta Syria.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 24, 2021
An Ceto Ma'aikata 11 Daga Wata Mahakar Zinari a China
-
Janairu 24, 2021
'Yan Sanda Sun Kama Dubban Masu Zanga Zanga A Rasha
-
Janairu 23, 2021
Adadin Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 a Duniya Ya Doshi Miliyan 100
-
Janairu 17, 2021
Wani Ayarin Baki Masu Kaura Na Dosar Amurka Daga Honduras
-
Janairu 16, 2021
India Ta Kaddamar Da Shirin Bada Riga Kafin COVID-19
-
Janairu 11, 2021
WHO Za Ta Aika Wata Tawagar Bincike China