Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Zama Wajibi Hada Kai Domin A Gudu Tare A Tsira Tare


Antonio Guterres

Yauce ranar majalisar dinkin duniya, ranar da aka kafa bayan yakin duniya na biyu wanda yakamata ya zama ranar hutu a kasashen duniya amma ba haka lamarin yake ba

Ranar 24, ga watan Oktoban kowace shekara de ranar ce wanda aka ware domin bikin ranar kafa majalisar ta dinkin duniya, kuma kudirin majalisar dinkin duniya ya bukaci kasashe mambobi a wannan majalisa dasu ayyana yau a matsayin ranar hutu a kasashen su sai dai kuma ba dukkan kasashen duniya ne ke bin wannan shawarar ba.

A irin wadannan kasashe ciki harda Najeriya, inda akasarin mutane basu san cewa yau ce ranar da aka ware domin majalisar ta dinkin duniya ba.

A sakonsa na bana Sakataren Majalisar dinkin Duniya Mr Antonio Gutiérres, yayi kira ga kasashen duniya da kuma al’umomi daban daban dasu hada kai domin magance matsalolin dake tunkarar duniya baki daya.

Yana mai cewa matakan magance wadannan matsaloli na hannun al’uma ne kuma da kasashe don haka kamata yayi ayi amfani dasu domin maganin matsalolin tun kafin lokaci ya ku’re, yace kasashen duniya na fuskatar balao’i daban daban ciki kuwa harda barazanar yaki na Nukiliya abinda kuma bai kamata ba.

Koda yake al’uma da dama basu san alfanun wannan rana ba, bikin na yau dai yazo ne a dai dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya, ta ware ranar 24, ga watan na Oktoba, a matsayin ranar wayar da kan al’uma akan amfani da kafofin yadda labarai da ake kira ”World Development Information Day” da nufin jawo hankalin al’umar duniya game da matsalolin da ake fuskanta wajen cigaban al’uma da kuma hanyoyin da za a bi na hada kai da juna domin a gudu tare a kuma tsira tare.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG