Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Abba Kyari Ya Ba Fadata Kariya – Buhari


Shugaba Buhari Ya gayyaci Matasa Shan Ruwa
Shugaba Buhari Ya gayyaci Matasa Shan Ruwa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yabi tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatinsa, marigayi Mallam Abba Kyari, kan yadda ya bai wa fadarsa kariya.

A karshen makon nan fadar ta sanar da rasuwar Kyari, wanda ya kwashe makonni yana jinyar cutar COVID-19 wacce ta yi sanadiyyar mutuwarsa.

A wani sakon ban-kwana da ya wallafa a shafinsa na Twitter @MBuhari a ranar Asabar, wanda ya yi wa taken “Zuwa Ga Abokina; Abba Kyari,” Buhari ya kwatanta marigayin a matsayin mutum mai kishin kasa, wanda ya ce bai gaza ba wajen bai wa fadarsa kariyar da ta dace.

“Kyari ya jajirce a matsayinsa na mai bai wa fadar shugaban kasa cikakkiyar kariya, inda ya tabbatar da cewa, ba a ba wani minista ko gwamna fifiko ba wajen shiga fadar.” Buhari ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Sakon ban-kwanan, ya kuma kara da cewa, “sannan ba a nuna banbanci tsakanin duk wadanda suke wakilta tare da yi wa kasarmu hidima ba.”

Tsakanin Abba Kyari Da Cin Hanci da Rashawa

Shugaban na Najeriya, wanda ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Kyari, ya bayyana marigayin a matsayin wanda bai damu da abin duniya ba.

“A maimakon haka, sai ya nesanta kansa da zamanin wasu ‘yan siyasar Najeriya, wadanda suka halalta cin hanci da rashawa, suka kuma mayar da mukaman siyasa tamkar hanyar cimma wannan buri.” In ji Buhari.

“Akwai wadanda suke cewa, Abba Kyari mutum ne mai zurfin ciki – saboda jama’a ba sa yabon sa. Amma Abba sabanin haka yake, domin ba ya bukatar mutane su yabe shi, saboda bai ga wani abu a cikin samun yabon mutane ba.”

“A fagen siyasa, Abba bai taba neman wani mukami ba.” Sakon Twitter na Buhari ya kara da cewa.

Alakar Buhari Da Kyari

“Shekarunsa sun haura 20 a lokacin da muka fara haduwa. Dalibi ne mai sanin ya kamata, ba da jimawa ba ya samu damar zuwa kasar waje domin karo karatu – farko a birnin Warwick sannan daga baya ya tafi jami’ar Cambridge inda ya karanci fannin shari’a.”

“Aminina ne cikin tsawon shekara 42, daga ya zama shugaban ma’aikatan fadar gwamnatina, kuma bai taba gazawa ba wajen ganin ya kyautatawa kowa da kowa.”

“Bayan da ya zama shugaban ma’aikatan fadar gwamnatina a 2015, ya gudanar da ayyukansu cikin nutsuwa ba tare da ya nemi an san shi ba ko yin wata cucuwa don gudanar da aikin da na sa shi ba.” In ji Buhari.

Mallam Abba Kyari ya rasu ne a ranar 17 ga watan Afrilu, 2020 yana da shekara 67 sanadiyyar cutar coronavirus, kuma cikakken dan Najeriya ne mai kishin kasa.”

“Ina mika sakon ta’aziyyata ga matarsa da iyalan da ya bari a baya bisa wannan babban rashi da kuka yi.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG