Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NOMA TUSHEN ARZIKI: Yadda Aka Gudanar Da Bikin Dalar Shinkafa A Jihar Kebbi - Maris 9, 2021


Mohammed Baballe

Daya daga cikin manufofin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shine bunkasa noman abinci ta yadda kasar zata wadata ta kuma iya ciyar da kanta da abinci.

Hakan ne ya sa shugaban ya kaddamar da shirin bayar da tallafin noma ga manoman shinkafa karkashin kulawar babban bankin Najeriya CBN a shekara 2015 a jihar Kebbi da ke arewacin kasar.

Dubban daruruwan manoma ne suka amfana da wannan shirin kuma suka tara shinkafa da yawan ta ya haura tan dubu dari biyu.

Wakilin Muryar Amurka Muhammad Nasir ya halarci bikin kaddamar da shinkafar, wadda ita ce ribar da shirin ya samu cikin shekaru biyar da fara shi. Ga dai yadda bikin ya kasance.

Yadda Aka Gudanar Da Bikin Dalar Shinkafa A Jihar Kebbi
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:45 0:00


XS
SM
MD
LG