ACCRA, GHANA - Bukin wannan shekarar ya samu halartar shugaban kasar Ivory Coast, Alhassan Ouattara, a matsayin babban bako, da jami’an diflomasiya.
Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo da yake jawabi a wurin bukin, a birnin Koforidua dake yankin Gabas ya ce, “Mu a Ghana mun san yadda za mu yi jagora.
"Mun yi hakan a shekarar 1957, lokacin da muka kasance kasa ta farko a Afirka a yankin Kudu da hamadar Sahara da ta samu ‘yancin kai daga kangin mulkin mallaka.
"A ko da yaushe muna samun nasarar fita daga yanayi masu wahala cikin alheri da ban mamaki. Mun dora wa kanmu da sauran kasashen Afirka ci gaba da samun dimokradiyyar da za mu yi alfahari da ita.
"Kuma mun dora wa kanmu da sauran kasashen Afirka bashin zama wadatacciyar al’umma, kuma za mu kai can”, a cewarsa.
Bayan Shugaba Akufo-Addo ya bayyana wasu nasarori da kasar ta samu a yayin da take gudanar da dimokradiyarta, ya kara da cewa, mulkin mallaka a asali ba shi da ka'idojin dimokradiyya, kuma “duk abin da muka sani game da zabe a yau, mun koya ne ta hanyar aiki tukuru, kuma a cikin shekaru talatin da ɗaya da suka gabata, mun kasance cikin kwanciyar hankali,” in ji shi.
Shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara ya yabawa Shugaban Ghana bisa kyakkyawar kwarewar jagoranci. Ya kara da cewa basirar shugabancin Shugaba Akufo-Addo ya tsallake Ghana har zuwa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS).
Sai dai wasu al’ummar Ghana sun bayyana ra’ayoyinsu game da bikin samun ‘yancin kan. Sun nuna cewa, babu bukatar bikin domin matsalar tsadar rayuwa da talauci da kuma rashin tausayin al’umma.
Shugaba Akufo-Addo ne dai ya juya bikin 'yancin kai na kasa zuwa yankuna daban-daban, don karfafa tattalin arzikin yankin.
Yankin Gabas shi ne yanki na uku da ya karbi bakuncin bikin bayan yankin tsakiya da kuma yankin Volta.
Dandalin Mu Tattauna