Wasu da suka halarci bikin sun bayyana cewa irin hadin kan da ya gudana a wurin bikin, zai kawo fahimtar juna da magance bambance-bambance tsakanin ‘yan Najeriya.
Kwamishinan yada labarai a jihar Plateau, Mr. Dan Manjang ya ce, bikin ya nuna cewa zaman lafiya ya samu a jihar.
Darakta janar na hukumar raya al’adun gargajiya ta kasa, Otunba Olusegun Runsewe ya ce, jihar Plateau ta kasance kamar manyan kasashe da ake tinkaho dasu wajen yawon bude ido.
Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya ce, bikin zai janyo hankalin duniya kan halin da ake ciki na annabar coronavirus da farfado da tattalin arzikin kasa.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji.