Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Gudanar Da Zanga-zangar Endsars A Legas, Abuja


Yadda aka gudanar da zanga zangar endsars a Abuja
Yadda aka gudanar da zanga zangar endsars a Abuja

Duk da gargadin da jami’an tsaro suka yi na hana taruwa a Lekki, hakan bai hana daruruwan matasa fitowa a ranar Laraba domin tunawa da wannan rana ba.

Tun da sanyin safiya ne dai rundunan ‘yan sanda a jihar Legas ta baza jami'an tsaro a manyan titunan birnin, musanman man ma dai shataletalen Lekki Toll Gate da ke zama dandalin gudanar da zanga zangar Endsars.

A ranar 20 ga watan Oktoba aka yi arangama da ‘yan sanda da masu zanga-zanga a bakin Lekki Toll gate a lokacin da guguwar endsars da ke adawa da rukunin ‘yan sanda na SARS ta barke.

Masu zanga-zanga sun yi zargin ‘yan sanda sun kashe wasu masu gangami a lokacin, zargin da hukumomin Najeriya suka musanta.

Sai dai duk da gargadin da jami’an tsaro suka yi na hana taruwa a Lekki, hakan bai hana daruruwan matasa fitowa a ranar Laraba domin tunawa da wannan rana ba.

A cewar Comrade Deji Adeyanju, daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar ya ce ko kadan ‘yan sanda ba su ikon hana su gudanar da zanga zangar lumana.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun kama wasu daga cikin masu zanga-zangar.

Sai dai kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas Waheed Odumasu ya ce, duk wanda ke da katin sheda da zai nuna cewa ba zauna gari banza ba ne a wajen wannan gangami an sake shi.

Yayin da wasu ke goyon bayan wannan gangami wasu kuwa na nuna adawa ne da shi inda wasu suka ce tarukan tunawa da rikicin na endsars bai kamata su gudana ba duba da yadda aka barnata dukiyoyin jama’a.

Kawo lokacin hada wannan rahoto dai komai na tafiya daidai a birnin na Legas, inda wasu ma ba su san abin da ake yi ba a wannnan bangare na birnin.

A birnin Abuja ma, masu zanga-zangar sun fita duk da cewa jami'an tsaro sun hana tarukan.

Masu zanga-zangar sun fara taruwa ne a dandalin Unity Foutain inda daga nan suka garzaya suka doshi majalisar dokokin kasar.

Rahotanni sun ce 'yan sanda sun datse masu boren yayin da suka tunkari ma'aikatar shari'a da ke Abuja.

Saurari cikakken rahoton Babangida Jibril:

Yadda Aka Gudanar Da Zanga-zangar Endsars A Legas, Abuja - 3'38"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00


XS
SM
MD
LG