Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Kalli Kusufin Rana A Wasu Kasashen Yankin Arewacin Amurka


Cikakken kusufi
Cikakken kusufi

Miliyoyin mutane ne suka kalli kusufin rana a wasu kasashe da ke yankin arewacin Amurka a ranar Litinin.

Kusufin ya ratsa tun daga kasar Mexico ya nausa Amurka ya kuma dangana da kasar Canada.

A Amurka, jihohin Vermont, New Hampshire da Maine da kuma New Brunswick a kasar Canada an ga wucewar kusufin na ranar wanda ya rufe baki daya a wasu yankuna.

Wannan shi ne kusufi mafi girma da ya taba aukuwa a yankin na arewacin Amurka a cewar masana.

A jihar New York, hazo ya dan kawo cikas ga masu kallon kusufin amma a jihar Texas da sauran wuraren da lamarin ya auku, an ga kufusin na dan wasu mintina yayin da wata ya ratsa ta tsakanin rana da duniyar dan adam.

Wani mutum sanye da tabarau din da ake kallon kusufu a Canada (APTOPIX Total Solar Eclipse Canada)
Wani mutum sanye da tabarau din da ake kallon kusufu a Canada (APTOPIX Total Solar Eclipse Canada)

Hakan ya sa yankunan da aka yi cikakken kusufin suka koma tamkar dare yayin da wuraren da aka yi rabi ya yi duhun yamma.

Kusufin rana kan auku ne a duk lokacin da wata ya shiga gaban rana ya kare haskenta ga duniyar dan adam.

Gabanin faruwar wannan al’amari, kwararru sun yi ta ba da shawarar yadda ya kamata jama’a su kalli wannan abin al’ajabi.

Hakan ya sa mutane da dama suka tanadi tabarau da kwararru suka amince da shi wajen kallon kusufin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG