Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Kona Motar Jonathan


Magoya bayan Shugaba Jonathan a Tafata Square, Janairu 8, 2014.

Rundunar tsaro ta “Special Task Force” a Jihar Filato ta cafke wasu matasa da take zargi da kona motar Bus, na yakin neman zaben Shugaba Goodluck Jonathan a titin Bauci road dake cikin garin Jos.

Kakakin rundunar tsaron, Kyaftin Ikedichi Iweha, ya tabbatar wa Muryar Amurka faruwar lamarin, inda ya kara cewa sun kama wasu matasa da ake zargi da cinnawa wani gida wuta, wanda a baya ake amfani da shi a matsayin caji Ofis na ‘yan sanda.

“Misalin karfe 6 da rabi zuwa 7 na yamma, muka samu rahoton cewa akwai motoci guda biyu da aka cinnawa wuta a titin Bauci Road, muka fara tambayoyi da bincike jiya. Akwai wadanda yanzu muke musu tambaya, kuma an bude titin da matasan suka rufe”, a cewar Kyaftin Iweha.

Wani wanda yaga abunda ya faru, kuma ya so a sakaye sunanshi, ya bayyanawa Muryar Amurka cewa:

“Abunda ya faru shine an biyo motar PDP zata wuce a Bauci road, dai-dai bakin gada, aka bi motar, da kyar direban ya tsira, ni bamu san yadda direban yayi ba, ita kuma motar aka cinna mata wuta, bamu san su waye sukayi wannan abun ba.”

“Mu dai babban dalilin da yasa muka je wajen, mun je wajen ne munga taro na jama’a, shine muka je mu bude hanya.”

Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tuntubi sakataren gudanarwa na Jam’iyyar PDP a Jihar Filato Micheal Dachum, cewa yayi motar da kyamfe din Shugaban Kasa ce, saboda haka basu da masaniyar daga inda ta fito, da kuma inda zata.

Kyaftin Ikedichi yace hukumar STF ta dauki matakan tabbatar da cewa kowa ya samu ‘yancin walwala, da bin hanyoyi ba tare da wata tsangwama ba.

XS
SM
MD
LG