Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Sallami Boris Johnson Daga Asibiti


Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson
Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson

An sallami Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson daga asibiti bayan da aka masa jinyar shu’umar cutar nan ta Coronavirus a dakin 'yan gobe da nisa.

To amma ba zai koma bakin aiki nan take ba, a cewar wata sanarwa daga ofishin Firai Ministan.

Sanarwar ta kara da cewa zai ci gaba da murmurewa a gidansa dake wajen gari.

Johnson ya kwanta a asibitin St. Thomas ne dake birnin Landan na tsawon mako guda, bayan kwana 10 da gano cewa ya kamu da cutar ta Coronavirus.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG