Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Sami Tsohon Frai Ministan Malaysia Da Badakalar Biliyoyin Daloli


Tsohon frai ministan Malaysia, Najib Razak
Tsohon frai ministan Malaysia, Najib Razak

A yau talata aka yanke wa tsohon Firai ministan kasar Malaysia Najib Razak hukunci bisa aikata laifuka 7 da ke da alaka da wawure miliyoyin kudin kasar dake asusun ci gaban kasa.

Babban Alkalin Kuala Lumpur, Mohammed Nazlan Mohammed Ghazali ya sami tsohon Firai Ministan dan shekara 67 da laifin amfani da mukaminsa ba bisa kaida ba, cin amanar kasa, da almundahana da kudaden kasa.

Masu gabatar da kara na kuma zargin Najib da karbar dalar Amurka kusan miliyan 10 daga wata kungiyar Kasa da kasa, SRC International.

Najib na fuskantar daurin shekaru 20 a gidan kaso akan kowane laifi daya da ake tuhumarshi, amma ya sha alwashin daukaka kara.

Najib Razak, tsohon frai ministan Malaysia
Najib Razak, tsohon frai ministan Malaysia

Najib na ikirarin cewa jami’an asusun na iMDB su suka yaudare shi har ya amince kudin da aka saka a asusun bankinsa gudumawa ce daga masarautar Saudiya.

Najib na kuma fuskantar tuhumar laifuka 42 tare da wadaqa da kudi dalar Amurka biliyan 4.5 daga asusun wanda shi ya kafa shi a shekarar 2009 domin farfado da tattalin arzikin kasar.

Masu bincike a Amurka sun ce an yi amfani da kudin ne wajen sayen otel otel da kayayikin alatu na alfarma kamar jirgin ruwa, kayan ado, da kuma daukar nauyin wanin shirin fim na Hollywood mai suna “Wolf of Wall Street.

Masu bincike na Amurka sun ce kudaden da suka shige a asusun bankin Najib sun kai wajen dala miliyan dubu.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG