Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Ake Zargin Masu Rike Da Madafun Iko Da Cin Zarafin Talakawa


Wani jami'in tsaro a Najeriya yayin da yake kan aiki
Wani jami'in tsaro a Najeriya yayin da yake kan aiki

Kundin tsarin mulkin Najeriya na cike da dokoki masu ma'ana da la shakka in an yi amfani da su, za su tabbatar da adalci da galabar masu amana kan maciya amana.

Kusan za a ce a Najeriya, mutane sun rabu zuwa kashi uku a matakin rayuwa da su ka hada da masu karfin mulki, masu karfin dukiya sai masu rayuwa da talauci.

Ba mamaki za a yi tunanin ai akwai masu ilimi ko fice kan wata sana'a; gaskiya wadannan na rayuwa ne a karkashin na farkon ka- tsaye ne ko a kaikaice.

Idan an koma ga batun jari hujja ajin mutanen ya kan koma biyu tsakanin masu hannu da shuni da talakawa!.

A jari hujja samfurin na Najeriya masu hannu da shuni da kan zama da karfin mukami ko abota da masu karfin iko kan zama a lokuta da dama sun fi karfin doka kuma ko an kai su kara zai yi wuya a iya hukunta su.

Wani zaman kotu a Najeriya
Wani zaman kotu a Najeriya

In ma an kara tsananta batun, wannan aji na jama'a su yi doka don haka ya ya doka za ta hukunta kan ta?.

Kundin tsarin mulkin Najeriya na cike da dokoki masu ma'ana da la shakka in an yi amfani da su, za su tabbatar da adalci da galabar masu amana kan maciya amana.

Ba sabon abu ba ne, ka ji gwamnati da kanta ba ta bin umurnin kotu amma da zarar kotu ta yanke hukunci kan muradinta, musamman na siyasa, za ka ga ta dau mataki nan take ta hanyar daure na daurewa ko firgita na firgitawa, da ma aikawa barzahu ga wanda kwana ya kare.

A nan, mu na son kawo wasu misalai na yadda 'yan jari hujja da masu kare kan murkushe doka hatta wajen mutunta danjar titi.

Direban tsohon gwamnan Akwa Ibom ministan Neja Delta a yanzu Godswill Akpabio ya saba dokar hanya daf da ofishin jakadancin Amurka a Abuja don ya na ganin mai gidansa wa imma ya fi karfin dokar titi ko ya fi kowa sauri a lokacin.

Nigeria 60th Independence Day President Muhammadu Buhari
Nigeria 60th Independence Day President Muhammadu Buhari

Wannan dalilin ya jawo mummunan hatsari da ya kai ga sauri ya haifi naw,a don sai da a ka garzaya da Akpabio ketare don neman magani da hakan ya sanya kashe makudan kudin al'umma da za a iya amfani da su wajen ayyukan raya kasa mafi muhimmanci, ga lamarin da in an bi doka za a iya kaucewa.

Ba wannan kadai ne misali ba. Shi ma kakakin majalisar dokokin Najeriya Femi Gbajabiamila ya haddasawa wani mai sayar da jarida tafiya lahira ba shiri.

Lamarin ya faru kan titi daf da majalisar dokokin ta Najeriya inda kakakin kan tsaya tun a shekarun baya ya gaisa da masu sayar da jaridar da yake ganin mutanensa ne har ya musu kyauta.

A ranar da akasin ya zo, daya daga cikin masu sayar da jaridar cikin sauran abokansa, sun nufo kwambar motocin Gbajabiamila wanda ya dan dakata don daga musu hannu.

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila

Can kuwa wani jami'in tsaron kakakin ya dauka haramun ne wani talaka ya tunkari maigidansa don haka ya bude wuta da nufin firgita masu sayar da jaridar su kauce don babban mutum da ba a zuwa kusa da shi ya wuce.

Sanadiyyar hakan, albarushi ya bugi daya daga cikin masu sayar da jaridar inda nan take ya riga mu gidan gaskiya.

A baya-bayan nan, wato a karshen watan Maris, wani hoton bidiyo da na’urar daukan hoto ta dauka a rukunin shaguna na Banex Plaza da ke Abuja, ya nuna shugaban kotun tabbatar da da’ar ma’aikata ta CCT yana jibgar wani matashin mai gadi, kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito.

Haka nan gadarar wani dan jari hujja a arewacin Najeriya tun can a shekarun 1980, ya taba jefo matarsa ta taga daga kan bene inda ta riga mu gidan gaskiya ba tare da ya yi nadamar abin da ya aikata ba tun da zai iya samun wasu matan da za su sadaukar da kansu gare shi don kwadayin abin duniya.

Wannan izza da wadanda su ka hau madafun iko su ke samu a Najeriya ya kara bayyana a watan Agusta na 2020 a Kalaba inda tsohon ministan zirga-zirgar jiragen sama ya ci zarafin wakilin jaridar"Daily Trust" kan tambayar wa ke daukar nauyin rangadin da ya ke yi a jihohin kusu maso kudu, inda Kayode ya kira dan jaridar da "wawa" kuma da ganin sa dama bai yi kama da masu tambaya ta basira ba.

Femi Fani-Kayode, tsohon ministan harkokin sufuri a Najeriya
Femi Fani-Kayode, tsohon ministan harkokin sufuri a Najeriya

Kayode ya yi ta ninkaya a tsananin fushi da nuna shi ba talaka ba ne da har wani zai tuhumi ta inda ya samu kudin rangadi.

Ala tilas, bayan tir da jama'a su ka yi da wannan dabi'a ta rashin daraja da ya yi, ya sa Kayode ya ce ya janye wannan kalami kuma hakan ba halinsa ba ne.

Shi ma Sanata Elisha Abbo daga jihar Adamawa ya share wata mata da mari har sau uku a wani shagon sayar da robobin jima'i a Maitama Abuja da kiran ta wawuya don neman kare abokiyar aikin ta da mujadala ta sarke a tsakanin su.

Ba don kamarar tsaro ta shagon ta dau lamarin ba, ba mamaki dan majalisar dattawan da ya musanta abin da ya aikata, don daga bisani ya ce sam hakan ba dabi'arsa ba ce kuma shi mutum ne mai karamci.

Wannan ya kai ga sai da kotu ta bi kadun matar Osimibibra Warmate da yanke hukuncin Abbo ya biya ta diyyar Naira miliyan 50.

Wani abin takaici daga 'yan jarin hujja a Najeriya shi ne yanda ba sa tsawatawa matuka kwambar motocinsu da kan ingije masu amfani da titi matukar ba su kauce gaba daya daga hanya ba in sun zo wucewa.

An sha samun jami'an tsaron masu rike da mukamai sun fasa gilasan motar wanda bai sauka daga titi ko ma auka rami ba sanadiyyar wadannan masu tunanin su shugabanni ne su na wucewa ta kan titi.

Motocin 'yan Sanda
Motocin 'yan Sanda

Wani lokacin ma jami'an tsaron kan juyo da baya su cafke wanda su ke ganin ya nuna taurin kai su kai shi wani waje a gidajen gwamnati su ma sa dukan kawo wuka.

Ba ma sai an kawo misalai na shugabanni a zamanin farar hula da soja ba da masu gadin kadai abun tsoro ne don yadda za su iya dirar mikiya kan kowaye, a kan gwamnonin da kan zundumawa kowa zagi su fatattaki talakawa daga gidan gwamnati wai da sunan a ranar ran su a bace ya ke ko kuma fassarar "Yau oga ba a daidai yake ba.”

Abin da ke bakunan mafi aksarin ‘yan Najeriya a kowane lokaci shi ne, yaushe doka za kasar za ta zama tsumagiyar kan hanya?

XS
SM
MD
LG