Da sammakon fara wasa Burnley ta zira kwallon farko cikin minti na biyar sai kuma kwallo ta biyu a minti na 10.
Johann Berg Gudmunsson ne ya fara zira kwallo farko sai Jay Rodriguez ya biyo da ta biyu a ragar Crystal Palace.
Wannan wasan farko da kungiyar ta yi nasara a wannan shekara.
Hakazalika ana dawowa daga hutun rabin lokaci Burnley ta zira kwallo ta uku a minti na 47, wacce Matt Lowton ya zira.
Akasi daya da Burnley ta samu shi ne kyaftin dinta Ben Mee da aka fita da shi daga filin wasa, bayan wani karo da suka yi da Jordan Ayew.
Ko da yake, kungiyar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, ya samu sauki.
Yanzu Burnley ta nesanta kanta da maki 11 daga shiga ajin ‘yan dagaji da za a fitar a daukacin gasar ta Premier.
Dubi ra’ayoyi
Ko ka yi rijista da mu? Shiga shafinka
Ba ka yi rijista da mu ba? Yi rijista
Load more comments