Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Coronavirus Ta Kashe Mutum 738 a Spain Cikin Kwana 1


Wani ma'akacin lafiya yayin da yake fitar da wata gawa daga asibiti a kasar Spain
Wani ma'akacin lafiya yayin da yake fitar da wata gawa daga asibiti a kasar Spain

Yanzu kasar kasar Spain ce ta fi kowacce kasa yawan mutanen da cutar Coronavirus ta kashe, idan aka dauke Italiya, bayan da mutum 738 suka mutu a kasar.

Yawan wadanda suka mutu cikin kwana guda ya sa adadin mutanen da suka mutu a kasar zuwa yanzu ya kai 3,434, wanda ya wuce yawan mace-mace 3,285 da aka samu a China.

Amma har yanzu kasar tana bayan kasar Italiya, wadda ke gaba a duniya da yawan mutanen da suka mutu 6,820.

Ma’aikatar lafiya ta Spain, ta fadi cewa karin wadanda suka kamu da cutar ya karu da kashi 20 cikin 100 daga ranar Talata zuwa 47,610.

Ma’aikatar ta ce mutane sama da 5,000 sun warke daga cutar a Spain.

Barkewar annobar dai ta nakasa tsarin kiwon lafiyar Spain, musamman ma a yankin Madrid, babban birnin kasar, inda aka sami kusan rabin wadanda suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG