Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Iyaye Ke Maida Hannun Agogo Baya A Yunkurin Dakile Yi Wa Yara Fyade


Masu ruwa da tsaki na bayyana damuwa akan yadda wasu iyaye da aka ci zarafin yaran su, musamman ta hanyar fyade ke saurin janye kararrakin neman hakki a gaban 'yan sanda ko kuma kotunan dake gudanar da shari'u akan irin wannan batutuwa, gabanin yanke hukunci.

KANO, NIGERIA - Hukumomi da kungiyoyin gwagwarmayar ‘yancin yara na ciki da wajen Najeriya sun himmatu wajen dakile ta'adar cin zarafin yara, musamman fyade ga yara mata, ta hanyar tsayin daka domin tabbatar da hukunci ga masu laifi.

Sai dai a hannu guda kuma, yadda galibin iyayen yaran da irin wannan abu ya faru da su suna yawan janye bukatun neman hakkin ‘ya’yan su avgaban kotu ko ofisoahin ‘yan sanda abinda ya zamana abin damuwa ga masu kokarin kwato masu hakki ko ‘yanci.

Barr Amina Umar ta reshen Jihar Jigawa na ofishin lauyoyin tarayya masu bada agajin kariya ga ‘yan kasa masu rauni ta fayyace wasu daga dalilan haka. Ta ce dalilan suna da yawa amma akwai guda biyu na musamman dake sa iyayen janye kararsu daga kotu.

Barrista Amina ta ce na farko shine tafiyar hawainiya da ita kanta bincike da shari’a suke yi, akwai kuma tsada Akan tafiyar da harkar irin wannan shari’a.

Bisa ga cewar ta, akwai kuma larurar jeka ka dawo na tilasta raunanan talakawa hakura da neman hakkin ‘ya’yan su, amma Barista Amina ta ce janye karar, hakan ba ita ce mafita ba.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Hukumomi Da Kungiyoyin Gwagwarmayar ‘Yancin Yara Sun Himmatu Wajen Dakile Cin Zarafi
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG