Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Filato Ta Bi Sahun Sauran Jihohi Wajen Garkame Kofofinta


Gwamnan Filato Simon Lalong
Gwamnan Filato Simon Lalong

Gwamnatin jihar Filato ta bayyana cewa za ta dinga rufe kan iyakokinta da suka hada da hanyar zuwa Bauchi da Abuja da jihar Nasarawa da kuma hanyar Zaria, daga karfe shida na yamma zuwa karfe bakwai na safe.

A taron manema labarai, sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Danladi Atu ya bayyana cewa dokar ta fara aiki ne daga ranar Lahadi, 29 ga watan Maris ta shekarar 2020 don dakile cutar Coronavirus.

Atu ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun gayyaci wani malami da ya jagoranci mutane zuwa sallar Jumma’a bayan dokar hana cunkoso da gwamnati ta kafa.

​Gwamnatin ta kara daukan wasu matakai na daban, kamar hana daukar mutane fiye da daya a cikin keke na pep.

Yayin da a motoci kuma mutum 4 ne za su iya shiga kawai, su kuwa motoci kirar bas mutum 7 ne za su iya dauka.

Saurari wannan rahoton a sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00


Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG