Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Korona Ke Shafar Rayuwar Wadanda Suka Kamu Da Cutar Bayan Sun Warke


Wani mutum ana yi mashi rigakafin Korona
Wani mutum ana yi mashi rigakafin Korona

Jami’an kiwon lafiya a Amurka sun fada jiya Laraba cewa, kusan 1 cikin 5 na Amurkawa manya da suka bada rahoton kamuwa da cutar COVID-19 a baya, har yanzu suna fama da alamomin COVID din na dogon lokaci, bisa ga bayanan bincike da aka tattara a cikin makonnin biyun farkon watan Yuni da ya gabata.

Bayanan sun nuna cewa, gaba-daya, 1 cikin manya 13 a Amurka suna da alamomin cutar COVID na tsawon watannin uku ko fiye bayan kamuwa da cutar ta farko, wadanda ba su da shi kafin su harbu.

Hukumar kula da cututtuka ta Amurka (CDC) ta yi nazarin bayanan da aka karba daga ranar 1 zuwa 13 ga wata Yuni, wanda hukumar kidaya ta Amurka ta yi.

Alamomin COVID da suke dadewa sun kama daga gajiya, saurin bugun zuciya, gajeren numfashi, matsalolin fahimta, ciwo mai radadi, tabin hankali da rashin kuzari. Suna iya zama masu rauni kuma suna iya daukan makonnin ko watanni bayan mutun ya warke daga ainihin kamuwa da cutar ta farko.

Wani binciken CDC kuma ya gano cewa matasa ta yuwu su fi dadewa da alamomin fiye da tsofaffi.

XS
SM
MD
LG