Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Kungiyoyin Kwadago Suka Fara Zanga-zanga A Biranen Najeriya


Zanga-zangar NLC a Abuja, babban birnin Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)
Zanga-zangar NLC a Abuja, babban birnin Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)

Zanga-zangar ta adawa ce da tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wadanda kungiyoyin suka ce sun jefa al'umar kasar cikin kangin rayuwa.

Gamayyar kungiyoyin kwadago ta NLC da ta hada da kungiyoyin ‘yan kasuwa ta TUC, sun kaddamar da zanga-zangar lumana a biranen Najeriya da dama a ranar Laraba.

Zanga-zangar ta adawa ce da tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wadanda kungiyoyin suka ce sun jefa al'umar kasar cikin kangin rayuwa.

Abuja, Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)
Abuja, Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)

Rahotanni sun ce tuni zanga-zangar ta kankama a jihohin Lagos, Filato, Kano, Kaduna, Imo, Abia, Benue, Enugu da Kwara.

Sauran jihohin da suke zanga-zangar sun hada da Ondo, Edo, Zamfara, Katsina, Rivers, Cross Rivers da Ogun.

Tun a makon jiya gamayyar kungiyoyin kwadagon ta ba da kashedin shiga wannan zanga-zanga wacce ke neman a sauke farashin litar man fetur a kuma maido da shirin tallafin man.

Zanga zanga a Kano (Hoto: Facebook/Auwal Zakari Ayagi)
Zanga zanga a Kano (Hoto: Facebook/Auwal Zakari Ayagi)

Jim kadan bayan rantsar da shi, Shugaba Tinubu ya janye kudin tallafin mai lamarin da ya sa litar mai ta tashi daga 189 zuwa 560 daga baya ta koma 617.

Shugaba Tinubu cikin wani jawbai na ba-za-ta da ya yi a ranar Litinin, ya nemi ‘yan kasar da su kara hakuri, inda ya zayyan wasu sabbin tsare-tsare da za su sawwaka rayuwar al’umar kasar.

Lagos, Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)
Lagos, Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)

Jawabin mataki ne na neman kungiyar ta NLC da TUC su janye zanga-zangar, kuma ga dukkan alamu sabuwar gwamnatin ta Tinubu ba ta kai ga gaci ba.

A baya, gwamnatin ta sanar da shirye-shiryen saukakawa 'yan Najeriya rayuwa wadanda har yanzu ba a fara aiwatarwa ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG